2 Satumba 2021 - 12:55
Najeriya : An Rufe Makarantu, Bayan Sace Dalibai 73 A Jihar Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara a najeriya ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu a fadin jihar, bayan da wasu ‘ya bindiga suka sace dalibai sama da 70 a jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara CP Ayuba Elkana a yayin da yake zanta wa da manema labarai a birnin Gusau, ya ce Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare a wani mataki na kyautata al'amuran tsaro a jihar.

Haka kuma CP Elkana ya ce gwamnan jihar ya bayar da umarnin sanya dokar hana fitar dare a dukkanin kananan hukumomin jihar 14.

Rahotanni dai sun ce dalibai 73 ne akayi garkuwa dasu bayan harin da ‘yan bindigan suka kai a makarantar dake kauyen Kaya a karamar hukumar Maradun.

Matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa na neman zama ruwan dare a Najeriya duk da ikirarin da hukumomi ke yi cewa suna daukar matakan takile al'amarin.

342/